Masar ta musanta zargin taya sojojin al-Burhan yaki a Sudan
October 10, 2024A wani faifan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna shugaban RSF Mohamed Hamdan Daglo na cewar sojojin saman Masar sun kai hari ta sama da zummar samun sojojinsa da ke kudancin Khartoum.
Daglo ya kara da cewar kasashe shidda ciki har da Iran ke fada da su a Sudan, a cewarsa Iran ta samarwa da sojojin gwamnati karkashin jagorancin Shugaba Abdel Fattah al-Burhan da jirage marasa matuka manya shida da ake yakin da su.
A wata sanarwa da ma'aikatar kasashen ketare ta Masar ta fidda ta nesanta kanta da duk wani zargin shiga rikicin na Sudan.
A watan Disambar shekarar bara kwararru da ke saka ido kan yaki a yankin Dafur sun gasgata sahihancin zargin da ake yi wa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa na taimaka wa sojojin Daglo da makamai.
Rikicin na Sudan ko baya ga hallaka daruruwan mutane a kuma jikkata wasu dubbai da matsugunnensu.
Karin Bayani:Bukatar isar da agajin gagawa a Sudan