1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta shiga wani hali na tsaka-mai-wuya

July 2, 2013

Shugaban Masar, Mohammed Mursi daga jam'iyar yan uwa musulmi, ya baiyana suka a game da wa'adin da sojoji suka baiwa masu hannu a rikicin kasar domin su warwre sabanin dake tsakaninsu.

Hoto: Reuters

Mursi ya baiyana haka ne a daidai lokacin da yake ci gaba da fuskantar zanga-zanga mai tsanani daga yan adawa da kungiyoyin dake neman kawar dashi daga mulki, saboda zarginsa da suke yi da laifin shimfida manufofi na jam'iyarsa mai bin akidar musulunci mai tsanai a kasar ta Masar.

Ko a yau ma, dubban yan zanga-zanga suka yi cincirindo a wani dandali dake kusa a babbar jami'ar birnin Alkahira da kuma dandalin yanci na Tahrir, domin ci gaba da adawarsu ga shugaba Mohammed Mursi. A wani titi dake kusa, yan zanga-zangar sun daga tutar dake nuna cewar wannan titi ne da aka haramtawa yan jam'iyar yan uwa musulmi su shiga. Masu lura da al'amuran yau da kullum suka ce wannan tuta ta zama wata alama ta yadda ake samun karkasuwa a Masar. A lokacin da aka fara juyin juya hali a Masar a watan Janairu na shekara ta 2011, yan Masar daga dukkanin addinai da dariku suka halara a dandalin Tahrir, domin nuna adawa da gwamnatin tsohon shugaba Hosni Mubarak, to amma a yau, shekaru biyu da rabi bayan wannan juyin juya hali, babu wani abin da ya nunar da wannan hadin kai. Masu adawa da shugaba mai ci, Mohammed Mursi ba ma suna neman ya aiwatar da gyare-gyare bane kawai, amma nema suke yayi murabus gaba daya daga mukaminsa, yayin da magoya bayansa, suke ci gaba da tsokaci da sakamakon zaben shugaban kasa da ya lashe, kuma suke cewar tilas ne yaci gaba da mulki a matsayin zababben shugaban kasa na halaliya. Gamal Soltan na jami'ar Amirka dake birnin Alkahira ya nuna cewar:

"Yanzu dai Masar ta rabu ne gida biyu. Yayin da jam'iyar yan uwa musulmi take son ganin addini ya taka muhimmiyar rawa a al'amuran yau da kullum na kasa, mafi yawan yan Masar basu da irin wannan ra'ayi, inda maimakon haka suke son ganin akida ko addininsu basu zama kan gaba a harkokinsu na yau da kullum ba. Wannan banbancin ra'ayi shi ya kai Masar ga halin da take ciki yanzu."

Zanga-zangar dake gudana yanzu, shekara guda bayan da Mohammed Mursi ya karbi mulki, ta zama abin da ke nuna rashin gamsuwa da manufofin siyasa na sugaban. Yan Masar da dama alal misali, sun nuna kyamarsu ga sabon kundin tsarin mulkin da aka fara aiki dashi tun daga watan Nuwamba na shekara ta 2012, saboda a bisa ra'ayinsu, sabon tsarin mulkin ya baiwa addinin musulunci matsayin da ya wuce kima a kasar. Hakan ya sanya mabiya sauran adinai ko akidodi, kamar yan yan Shia ko Kirista yan darikar Coptic suke ganin an maida su saniyar ware. Rashin gamsuwa da mulkin Mohammed Mursi a fannnin siyasa, ya kuma kara tsananta sakamakon matsalolin da Masar take fama dasu yanzu a fannin tattalin arziki. A sakamakon shawarwari da hukumar kudi ta duniya, Masar tayi alkawarin aiwatar da canje-canje masu tsanani a fannin tatalin arzkin, misali ta hanyar rage kudaden da gwamnati take shigarwa domin rage tsadar kaya da kuma sanya karin haraji kan yan kasa, wadanda duka abubuwa ne da suka sanya jam'iyar yan uwa musulmi dake mulki tayi asarar goyon bayanta tsakanin jama'a. Duk da haka, kamar yadda Ahmed Kamaly, na jami'ar Amirka a birnin Alkahira ya nunar, babbar matsalr Masar dai na siyasa ne.

Kiristoci yan darikar Coptic suna ganin an maida su saniyar wareHoto: picture-alliance/Arved Gintenreiter

"Yace Masar babbar matsalarta ta shafi yanayin siyasa ne a kasar. Yan kasa suna zaune cikin yanayi na rashin tabbas, saboda masu rike da manyan mukamai basa nuna alamn sun kware wajen tafiyar da aiyukansu. Idan har aka sami kyautatuwar yanayin siyasa, babu shakka tattalin arzikin kasar ma zai bunkasa. Saboda haka ne abin da yan Masar suke bukata cikin gaggawa shine kwanciyar hankalin siyasa, idan kuwa ba haka ba, babu fatan samun haske garesu nan gaba kadan."

Wannan kwanciyar hankali na siyasa da alamu ba zai samu kamar yada shugaba Mohammed Mursi yake bukata ba, domin a tsakiyar wannan rikici ne akalla ministocinsa shidda, cikinsu har da ministan harkokin waje, Mohammed Kamal Amr suka yi murabus.

Shugaban Masar Mohammed MursiHoto: Imago

Mawallafi: Knipp/Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal