Masar ta tsoshe kafofin Internet 60
June 12, 2017Talla
A tun karshen watan Mayu da ta gabata ne hukumomin kasar suka fara toshe kafofin yada labarai ta Internet na aksashen waje da na cikin gida guda 20. Cikin wadan da abin ya shafa, akwai kamfanin yada labaran kasar Masar mai zaman kanta wato Mada Masr da kuma kamfanin Al-Jazeera reshen ta da ke Masar.
Ana dai zargin wasu shafukan da caccakar manufofin gwamnati da ma sukar ayyukan cin hanci da rashawa a cikin kasar, sai dai kawo yanzu bangaren gwamnati ba su ce komai a kan toshe wadannan kafofin yada labarai ba.
Alkaluman da kungiyar da ke fatutikar kare 'yan jarida a duniya "Reporters without Borders" ta wallafa a wannan shekara, na nuna kasar Masar a jerin kasashe na 161 cikin kasashen 180 dake mutunta 'yancin albarkacin baki a fadin duniya.