Masar ta yanke dangantaka da Siriya
June 16, 2013Da ya ke jawabi ga wani taron muzahara da malaman Sunna su ka kirawo a kasar, Mursi ya kuma bukaci kungiyar Hezbollah ta Labanon ta daina sanya baki cikin yakin na Siriya.
A nata bangaren Rasha da ke zaman babbar kawa ga gwamnatin Siriya, cewa ta yi duk wani yunkuri na sanya takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama a Siriya ya saba wa doka.
Da ta ke maida martani kan jawabin na Mursi gwamnatin Siriya, ta yi tir da matakin da ya dauka na yanke hulda da Damaskus din, da kuma nuna goyon bayansa ga shirin kakaba mata takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama da baiwa 'yan tawayen da ke yakar gwamnatin Bashar al-Assad kananan makamai, suna mai cewa hakan wani mataki ne da bai da ce ba.
Mawallafiya : Lateefa Jaafar Mustapha
Edita : Zainab Mohammed Abubakar