Masar ta yanke wa mutane 28 hukuncin kisa
July 23, 2017Talla
Kotun wadda ke birnin Alkahira, ta kuma yankewa wasu 38 daga 'yan ta'addan hukuncin daurin da ya kama daga shekaru 10 zuwa zama na rai-da-rai. 16 daga cikinsu har ila yau an yanke masu hukuncin ne ba tare da sun kasance a wajen ba.
Cikin watan Yunin shekara ta 2015 ne dai 'yan ta'addan suka kashe Hesham Barakat, a wani harin bam da suka kaddamar kusa da gidansa da ke Alkahira. Daga cikin hukuncin da aka yanke masun, har da na laufin mallakar nakiyoyi da hada kai da kungiyar Hamas da ta kasance sanadin kafuwar kungiyar Muslim Brotherhood da ta ke kai hare-hare a kasar.