Masar tana ci gaba da fuskantar rikicin siyasa
July 16, 2013Jami'an tsaron kasar Masar sun yi fito-na-fito da magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Mursi tun cikin daren wannan Litinin (15.07.13) zuwa sanyin safiyar wannan Talata (17.07.13).
Tashin hankalin ya samo asali ne lokacin da masu zanga-zangar suka yi yunkurin toshe babbar gadar kogin Nilu. Masu zanga-zangar sun yi amfani da duwatsu wajen jifar 'yan sanda, wadanda suka mayar da martani ta hanyar watsa hayaki mai-saka hawaye, akwai kimanin mutane 22 da suka samu raunuka.
'Yan kungiyar 'yan Uwa Musulmai sun nemi janar Abdel Fattah al-Sisi wanda ya jagoranci juyin mulki ya yi murabus daga aikin soja, sannan a mayar da Mursi kan madafun iko. Duk wannan lamarin na faru wa ne yayin da mataimakin sakataren harkokin wajen Amirka William Burns ya gana da sabbin mahukuntan kasar ta Masar.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh