Masar tana ci gaba da kai farmaki kan tsageru a Libiya
February 16, 2015Talla
Kasar Hadaddiyar Daular Laraba ta bai wa kasar Masar goyon baya bisa hare-haren da ta kaddamar kan kungiyar neman kafa daular Islama ta kasar Libiya, bayan mayakan kungiyar sun hallaka 'yan kasar ta Masar 21 Kiristoci mabiya darikar Coptik.
A wannan Litinin rahotanni sun nuna cewa jiragen saman yakin kasar ta Masar sun ci gaba da luguden wuta kan wuraren da ake zargin mayakan da suka hallaka 'yan Masar suna buya. Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya nuna bakin-ciki da kisan da aka yi wa 'yan kasar ta Masar. Tuni mahukuntan Masar suka nemi kawancen da Amirka ke jagoranta da suka kai farmaki kan mayakan IS na Libiya.