1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Yanayi

Taron sauyin yanayi COP27 a Masar

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 10, 2022

Kananan manoma na kasashen yankin Kudu da Saharar Afirka da na yankin kudancin Asiya wadanda ke fama da radadin tasirin sauyin yanayi, sun samu tallafin dalar Amirka biliyan daya da miliyan 400.

Masara | Sharm El-Sheikh | COP27 Logo
Kasar Masara na karbar bakuncin taron sauyin yanayi na COP27Hoto: Mohammed Abed/AFP

Tallafin kudin da ya fito daga gidauniyar Bill da Melinda Gates za a rarraba shi ne cikin tsawon shekaru hudu, kuma an  ware shi domin gaggauta bullo da matakan tunkarar matsalolin sauyin yanayi da suka hada da fari da tsananin zafi da ambaliyar ruwa. Wata sanarwar da aka fitar, yayin taron sauyin yanayi na COP27 da ke gudana a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh na kasar Masar ce ta bayyana hakan. Wasu kungiyoyi da ke wakiltar iyalan manoma har miliyan 350 sun mika wata budaddiyar wasika ga shugabannin duniya yayin taron, inda suke gargadin tsunduma cikin matsalar karancin abinci a duniya muddin gwamnatoci suka gaza wajen samar da kudin bunkasa albarkatun gona ga kananan manoma.

A nasa bangaren sakataren janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya nuna damuwarsa ga rahoton da masana yanayi suka gabatar, wanda ke nuni da karuwar dumamar yananyi da a bana har yakai ga sama da maki daya a ma'aunin celsius. Guterres ya yi suka ga irin son kan da kasashe masu galihu da ke zama musabbabin dumama ko sauyin yanayin da duniya ta tsinci kanta a ciki ke nunawa, wajan tabuka abun da zai rage dumamar yanayin da tallafawa kasashe marasa galihu. Sai dai duk da haka, ya yaba da yunkurin da kungiyoyi masu zaman kansu ke yi a wannan bangaren.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani