1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Masar za ta dauki nauyin taron sasanta rikicin Sudan

May 29, 2024

Kasar Masar za ta karbi bakwancin wani taro a kan Sudan, taron da ake sa ran samun halartar wakilan kungiyoyi na kasar da ma wasu daga kasashen duniya.

Janar al-Burhan na Sudan da Shugaba al-Sisi na Masar
Shugaba al-Burhan na Sudan da Shugaba al-Sisi na kasar MasarHoto: Egyptian Presidency/AP/picture alliance

Babban burin taron da za a yi cikin watan gobe, shi ne samun yarjejeniyar samar da dawwamammen zaman lafiya da zai kawo karshen rikicin da Sudan ta fada a ciki.

Tun cikin watan Afrilun bara ne dai kasar ta Sudan ta fada yakin basasa, sakamakon takaddamar siyasa tsakanin sojojin kasar karkashen Shugaba Abdul Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo.

Dubban fararen hula ne dai aka yi kiyasin sun salwanta kawo i yanzu a kasar.

Muhimman kasashe Irin su Amurka da Masar da ma Saudiyya, sun yi ta kokarin samar da masalaha kan rikicin na Sudan amma lamarin ya ci tura.