1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Masar za ta shirya taro kan makomar Gaza

October 11, 2025

Masar za ta jagoranci taro kan Gaza, bayan fara aiwatar da shirin Trump na kawo karshen yaki tsakanin Isra'ila da Hamas.

Dubban Falasdinawa da ke rububin komawa cikin buraguzan gidajensu a Gaza
Dubban Falasdinawa da ke rububin komawa cikin buraguzan gidajensu a GazaHoto: Mahmoud Issa/REUTERS

Hukumomin Masar sun ce Shugaban Amurka Donald Trump shi ne zai kasance babban bako a wajen taron tare da takwaransa na Masar Abdel-Fattah al-Sissi.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce tuni Ministan Harkokin Wajen Kasar Badr Abdel-Atti da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio suka fara tattaunawa ta wayar tarho domin fara aiwatar da daftarin gudanar da taron.

Karin bayani:Masar ta shirya taron zaman lafiya kan rikicin Gaza 

Shugabannin kasashen yammacin duniya da dama ne ake sa ran zasu hakarci taron na Masar kan Gaza. Kazalika Shugaba Al-Sissi ya gayyaci Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz domin ya shaida aiwatar da yarjejeniyar.

Karin bayani: Isra'ila ta amince da tsagaita wuta a yakin Gaza

A wani labarin kuma babban kwamandan rundunar tsaron Amurka ya isa Gaza, inda ya tabbatar da cewa babu wani sojin Amurka guda da ke yankin.