1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

Shugaban Masar na shirin yin tazarce

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 8, 2023

Al'ummar kasar Masar na shirin fita rumfunan zabe a karshen mako, domin gudanar da zaben shugaban kasa da ake kyautata zaton shugaban kasar mai ci Abdel Fattah al-Sisi zai yi nasarar yin tazarce a karo na uku.

Masar | Abdel Fattah al-Sisi | Zabe | Tazarce
Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na kasar MasarHoto: Michael Kappeler/AFP/Getty Images

Babban zaben na Masar dai na zuwa ne, a daidai lokacin da kasar ke cikin matsanancin hali na masassarar tattalin arziki da ke zaman mafi muni da ta taba shiga. Al'ummar kasar Masar din daga shekaru 18 zuwa sama za su kada kuri'unsu a rumfunan zabe 9,400 da aka ware har tsawon kwanaki uku, a zaben da 'yan takara uku ke shirin fafatawa da shugaban kasar mai ci yanzu Abdel Fattah al-Sisi da ke kan karagar mulki tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta marigayi Mohamed Morsi a shekara ta 2013.