Maslaha ga rikicin Sabiya da Kosovo
August 4, 2011Ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO dake gudanar da aiki a Kosovo, ta tsara yarjejeniyar cire ɗaukacin shingayen da aka dasa a arewacin yankin. Ƙungiyar ƙawancen tsaron NATOn dai ta ce za'a kawar da ɗaukacin shingayen da aka ƙafa a yankin kan iyakar da sasan biyu ke taƙaddama akan sa, kana dakarun ta ne za su ci gaba da yin sintiri a wurin.
Yarjejeniyar, wadda NATOn ta cimma tare da ƙasar Sabiya, hukumomin yankin Kosovo sun sanya ƙafa sun shure ta. Mahukunta a birnin Pristina na yankin Kosovo sun nuna rashin jin daɗin su game da yarjejeniyar, domin kuwa suna ƙaunar ganin sun ci gaba da katse duk wani matakin shigowa da kayayyaki ta kan iyaka daga Sabiya. A watan jiya ne dai hukumomin Kosovo suka haramta shigo da kayayyaki daga Sabiya, a matsayin martani ga kwatankwacin matakin da mahukunta a birnin Belgrade na ƙasar Sabiya suka ɗauka tun a shekara ta 2008.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas