Mastayin Jamus da Faransa kan bashin Girka
August 25, 2012Da ya ke ganawa da jaridar Tagesspeigel ministan harkokin kuɗin Jamus Wolfgang Schaeuble ya ce ƙarin wa'adi ga girka na nufin ƙara mata kuƙi wanda kuma ke nufin ba ta wani sabon tallafin ceto.
Minista Schaeuble ya kara da cewar ɗaukar wannan mataki na sake tallafawa Girka ba hanya ce mai bullewa musamman idan aka yi la'akari da warware matsalar tattalin arzikin da kasashsen da ke amfani da kuɗin bai daya na euro ciki har da Girkan su ka tsinci kan su a ciki.
Ita ma dai kasar Faransa wannan matsayi ta ɗauka kamar yadda shugabanta Farncois Hollade ya shaida a wata hira da manema labarai inda ya ce Girka za ta cigaba da kasancewa a ƙungiyar da ke amfani da kuɗin bai daya na euro amma fa ya zama wajibi Girkan ta zage damtse wajen ganin ta aiwatar da gyare-gyaren da su ka dace don samun sukunin fidda kitse daga wuta.
Shugaba Hollande ya yi wadannan kalamai ne yayin da Priyiministan Girka Antonis Samaras ya ziyarce shi, kwatankwacin ziyarar da ya kai Jamus.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh