1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu adawa da gwamnati a Thailand sun gabatar da wasu sharuɗa

April 24, 2010

Masu sanye da jajayen rigunan sun ce zasu kawo ƙarshen zanga zangar idan gwamnati ta amince za ta rushe majalisar dokoki cikin kwanaki 30.

Dubban masu zanga zangar adawa da gwamnatin Thailand a birnin Bangkok,Hoto: AP

Masu adawa da gwamnati a ƙasar Thailand waɗanda ke sanye da jajayen riguna sun ƙara jan damarar tunkarar wata gagarumar fito na fito dangane da dirar mikiya da jamián tsaro ka iya yi musu domin kawo ƙarshen zanga zangar nan da saoi 48 bayan da Firaministan yayi fatali da buƙatarsu ta kiran zaɓe gabanin waádi a matsayin masalaha. Masu jajayen rigunan dai sun ce zasu kawo ƙarshen zanga zangar da suka shafe tsawon makonni suna yi idan gwamnatin ta amince zata rushe majalisar dokoki cikin kwanaki 30 ta kuma gudanar da sabon zaɓe a cikin kwanaki 90. Masu zanga zangar dai magoya bayan tsofon Firaminista ne Thaksin Shinawatra waɗanda a yanzu haka suke cigaba da mamaye wuraren harkokin kasuwanci a birnin Bangkok. A waje guda rahotanni na cewa aƙalla mutum guda ya rasu yayin da wasu mutanen kimanin 90 suka sami raunuka a arangama da jamián tsaro. 

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

  Edita : Zainab Mohammed Abubakar