1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Masu adawa da Isra'ila sun mamaye bikin fina-finan Venice

August 27, 2025

Daruruwan mutane suka gudanar da zanga-zanga a harabar dandalin bikin fina-finai da ake yiwa lakabi da Venice Film Festival, domin nuna adawa da mamayar da Isra'ila ke yi a Gaza.

Daraktan shirya bikin fina-finan Venice Film Festival Alberto Barbera a yayin zanga-zangar neman hakkin mata a Iran
Daraktan shirya bikin fina-finan Venice Film Festival Alberto Barbera a yayin zanga-zangar neman hakkin mata a IranHoto: Vianney Le Caer/Invision/AP/picture alliance

Masu zanga-zangar dauke da allunan da ke cewa ''a tabbatar da 'yancin Falasdinu' da kuma 'kawo karshen kisan kare dangi a Gaza' da makamantan rubuce-rubuce sun yi cincirindo a dandalin gudanar da bikin fina-finan Venice na Italiya, inda al'amura suka tsaya cak!

Karin bayani:Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Yemen

Fim din da aka shirya kan rayuwar wata yarinya 'yar shekara shida mai suna Hind Rajab, da sojojin Isra'ila suka halaka a 2024 na daga cikin fina-finan da suka shiga gasar samun lambar yabo ta 'Golden Lion' a gasar ta bana, kamar yadda daraktar da ta shirya fim din Kaouther Ben Hania ta sanar da manema labarai.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW