1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu adawan Siriya na cigaba da nuna turjiya

August 2, 2011

Masu adawa a Siriya sunce za su cigaba da gudanar da zanga-zanga a kowani daren wannan watan na Ramadana

Hoto: picture alliance/dpa

Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ta gana da daren jiya a asirce domin tattauna ta'azaran da rikicin Siriya ke yi. Wannan ganawa dai ta biyo bayan rahotannin da suka fito daga Siriyan waɗanda ke zargin jami'an tsaron ƙasar da aikata kisar gilla a kan masu zanga-zanga. Masu fafutukar kare haƙƙin bil adama sunce aƙalla mutane 100 suka hallaka bayan da Jami'an tsaron suka kai hari da tankokin gwamnati ranar lahadi, a yayin da wasu bakwai kuma suka rasu a jiya litini. Shugabanin Tarayyar Turai da na daga cikin waɗanda suka yi kira da Kwamitin Sulhun da ya gudanar da wannan tattaunawar da fatar cewa ganawar zata kai ga ɗaukan matakan shawo kan rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Kawo yanzu dai mambobin kwamitin guda 15 sun kasa cimma matsaya dangane da matakin da ya kamata su ɗauka. A nasu ɓangaren dai masu boren nuna ƙyaman gwamnatin, sun sha alwashin gudanar da zanga-zanga a titunan ƙasar a kowani daren wannan wata na Ramadanan.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu