1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu boren Siriya na cigaba da nuna turjiya

June 18, 2011

Dakarun da ke biyayya ga shugaba Bashar al-Assad na Siriya sun kutsa zuwa ƙauyen Bdama

Wasu 'yan gudun hijira daga SiriyaHoto: dapd

Wadanda suka gane wa idanunsu a arewacin Siriya, sunce dakarun da ke biyayya ga shugaba Bashar Al-Assad sun mamaye ƙauyen Bidama wanda ke kan Iyakar ƙasar, sun kuma ƙona gidaje sun cafke fararen hula kana sun yiwa da dama rauni. Rahotanni sun nuna cewa dakarun na Siriya sun kashe mutane fiye da 130, kuma suna riƙe da kimanin wasu 2,000 a yankin Yisir Al Shukur a 'yan kwanakin baya-bayan nan.

A jiya juma'a dubun dubatan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Siriya suna nuna adawa da fatattakar da dakarun Assad ke gudanarwa. Masu boren da kafafin yaɗa labarai sun bada alƙalumma mabanbanta na waɗanda suka yi rauni. To sai dai masu fafutukar kare haƙƙin biladama sun ce rikicin ya fi muni ne a garin Homs wanda ke da kimanin mazauna milliyan ɗaya. Jami'ai a Turkiyya sun ce masu gudun hijira fiye da dubu 10 sun ƙetara zuwa ƙasar Turkiyyan kuma wasu dubu 10n na jira a iyakar ƙasashen biyu.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Ahmad Tijani Lawal