1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu bukata ta musamman na son kulawa

Binta Aliyu Zurmi
May 6, 2020

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci gwamnatocin kasashen duniya da su yi la'akari da dubban mutane masu bukata ta musamman a fafutukar da suke yi ta kawo karshen annoba Corona

Coronavirus - UN-Generalsekretär Guterres
Hoto: picture-alliance/dpa/Keystone/C. Zingaro

Babban sakataren ya baiyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya nuna goyon baya ga wani nazari da Majalisar Dinkin Duniyar ta gudanar kan mutane masu bukata ta musamman.

Mr Guterres ya ce annobar corona ta kara samar da wagegen gibi na rashin daidaito da haifar da sabbin barazana.

Ya kara da cewa ko a lokacin da hankalin duniya ke kwance ire-iren wadannan mutane masu bukata ta musamman akan manta da su, wanda hakan ke tauye musu hakkin samun ilimi da ingatancen tsarin lafiya da ma damar bada tasu gudumawa a yankunansu.