1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan jihadi sun toshe wasu hanyoyin shigar da kaya Mali

September 11, 2025

Hukumomin mulkin sojin Mali sun musanta girman wannan lamari da wasu ke cewa ya fara yin illa ga harkokin kasuwanci da kuma walwalar jama'a musamman a yammacin kasar.

Shugaban mulkin sojin Mali
Shugaban mulkin sojin MaliHoto: OUSMANE MAKAVELI/AFP/Getty Images

Rahotanni daga Mali na cewa a 'yan kwanakin nan kungiyoyin dake da'awar jihadi sun toshe hanyoyin da ke sada yankunan kudanci da kuma yammacin kasar da kasashen Senegal da kuma Mauritaniya, hanyoyin da ke da matukar mahimmanci wajen shigo da kayayyakin amfanin yau da kullum.

Karin bayani: Senegal ta haramta amfani da babura a kan iyakokinta da Mali 

Hakazalika tun daga farkon wannan wata na Satumba mayakan jihadin na Mali sun kuma ringa kafa shingaye a lokaci zuwa lokaci a kan hanyoyin da ke zuwa Bamako babban birnin kasar, lamarin da ya haifar da cikas ga zirga-zirgar mutane da kuma hajoji.

Shaidun gani da ido da dama sun ce sun ga dogon layin motoci da aka dakatar a kan babbar hanyar Segou zuwa Bamako, sannan kuma 'yan jihadin sun kona akalla motocin jigilar mutane sama da guda 10 a kwanakin nan.

Sai dai hukumomin mulkin sojin Mali sun musanta girman wannan lamari da masu sa ido kan al'amuran yau da kullun suka ce ya fara yin illa ga harkokin kasuwanci da kuma walwalar jama'a musamman ma a yammacin kasar.