1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin masu corona zai haura miliyan goma

Abdourahamane Hassane
June 24, 2020

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a kwanaki na gaba za a kai adadi mafi girma na wadanda suka kamu da cutar covid 19 a duniya yayin da har yanzu cutar ba ta kai kololuwarta ba a yankin Latin Amirka.

Ausbruch von COVID-19 in Gütersloh
Hoto: picture-alliance/AP Images/M. Meissner

Tedros Adhanom Ghebreyesus daraktan hukumar lafiyar ta duniya WHO shi ne ya bayyana wannan sanarwa a wani taron manema labarai da ya kira: ''Muna tsamanin kimanin mutane miliyan goma za su kamu da cutar corona a makon gobe. Wannan wani labari ne marasa dadi, ko ma dai muna ci gaba da neman maganin cutar ya zama wajibi mu dauki matakan kare rayuwar al'umma.''