A kokarin neman mafita daga wahalhalun tsadar rayuwa da karin farashin man fetur ya jawo musamman a bangaren sufuri da kuma ga masu matsakaita da kananan masana'antu, wasu masana sun kirkiro da fasahar sauya man fetur da gas wajen sarrafa ababan hawa da na'urorin sana'o'i.