1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masu kwarmata bayanai na fuskantar hadari a Afirka

September 3, 2024

Masu fallasa bayanan almundahana da satar dukiyar gwamnati a kasashen Afirka na ci gaba d fuskantar barazana ga rayukansu.

Kenia Pressefreiheit | Demonstration gegen ein Mediengesetzt in Nairobi
Hoto: Xinhua/IMAGO

A kusan galabin kasashen Afirka ne dai, masu fallasa almundahana ke fuskantar barazana. Kisan gillar da aka yi wa dan jarida mai binciken kwakwaf a kasar Ghana Ahmed Suale na daga cikin manyan misalan lahanin da ake zargin masu iko na yi wa mutanen da ke kokarin fallasa barnar da ake zarginsu da aikatawa. A shekara ta 2019 ne dai aka bindige dan jarida Suale bayan da rahotonsa ya bakantawa dan majalisa Kennedy Agyapong rai a badakalar da aka tafka a hukumar kwallon kafar Ghana. Dan jarida Manasseh Azure Awuni wanda binciken kwakwaf din da ya ke yi a Ghana ya tilasta masa yin hijira zuwa Afirka ta Kudu a 2020, yanzu ya dawo Ghana amma ba ya iya yawo ba tare da jami'an tsaro ba. Ya shaida wa DW girman barazanar da yake fuskanta.

Taron 'yan Jarida masu binciken kwakwaf a Afirka ta KuduHoto: Million Haileselassie/DW

"Abubuwan da ake mana na haddasa mana ciwon damuwa na kwakwalwa. Hakan yana nuna hatsarin da ke tattare da aiki a muhallin da ake maka barazana, za a iya kashe ka, daga karshe a hana ka samun bacci bisa yawaitar barazanar kisa. Amma mu masu fallasa bayanan nan, idan har abun da muke aiki a kansa ya shafi ci-gaban kasa, babu yadda za mu yi kasa a gwiwa.''

Ba a kasar Ghana kadai irin hakan ke faruwa ba, amma abin da yake da daure kai a Ghana shi ne kasar na da dokokin da suka samar wa masu fallasa barna da dukiyar al'umma kariya. Yayin da gaba daya kasashen Afirka ban da Eritrea suke cikin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ta fallasa masu cin hanci da rashawa, kasashe 10 da suka hada da Cape Verd, Djibouti, Kongo, Maroko, Mauritaniya, Somaliya, Sudan ta Kudu, Eswatini, sun ki rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Alamar kwarmata bayanan sirriHoto: Andrey Popov/Panthermedia/imago images

A gefe guda kuma, mutanen Afirka ta Kudu ba su mance kisan da aka yi wa Babita Deokaran, wanda ke cikin manyan shaidun yadda aka tafka almundahana da kudin sayo kayan yaki da  corona a 2021  ba. Wannan lamari ya sanya  Elijah Kandie Rottok, babban jami'i a hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Kenya bukatar gaggawa ta samar da kariya ga mutanen da ke son daga murya da ma bankado wadanda ke kwasar dukiyar l'umma.

"Aikinmu ne a matsayinmu na 'yan Afirka ko kuma gwamnati mu karfafi gwiwar wadanda ke fallasa barna, mu kuma dauki matakin kare su daga duk wani mugun abu idan har da gaske muke muna son inganta aikin gwamnati da tabbatar da gaskiya.''

'Yar Jarida Mariama Soumana Hassane a NijarHoto: Ali Mamadou

Barazanar da ake yi wa masu binciken kwakwaf din dai har yanzu ba ta cika tsorata su ba, inda a baya-bayan aka samu wani dan jarida da ake wa lakabi da Dan Bello da shi ma ke ci gaba da bankado zarge-zarge na cin hanci da ma almundahana a arewacin Najeriya. Shin me ya sa suke ci gaba da bayyana a kusan kowane yanki na Afirka duk da hatsarin da ke tattare da bankade-bankaden barnar aikin gwamnati? Dan jarida  Awuni na kasar Ghana ya yi karin bayani, inda ya ce yana ganin hakan a matsayin gudunmawar da zai iya bayarwa ga habbaka salon mulkin dimukuradiyya a kasar Ghana da ma samar da ci-gaban kasarsa.

 A yanzu masana na cewa kallo ya koma kan 'yan majalisun kasashen Afirka da su yi dokoki a inda babu su tare da tabbatar da aiwatar da dokokin a kasashen da ke da su a rubuce cikin takarda da zummar samar da kariya ga mutanen da suka zabi tsage gaskiya komai dacinta.