1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masu rikici da juna a Sudan na tattauna batun tsagaita wuta

Mouhamadou Awal Balarabe
July 12, 2024

Majalisar Dinkin Duniya na neman shawo kan sojojin Sudan da dakarun RSF don su daina barin wuta da nufin kare rayukan fararen hula da shigar da kayan agaji a kasar da ke fama da yaki.

Wakilan bangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun saba tattaunawa a Masar
Wakilan bangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun asaban tattaunawa a MasarHoto: Ibrahim Mohammed Ishak/REUTERS

Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun gudanar da tattaunawa a birnin Geneva kan batun kare fararen hula da tabbatar da isar da kayan agaji a kasar. Majalisar Dinkin Duniya wacce ke shiga tsakanin sojojinSudan da dakarun sa kai na RSF ta ce abokan gaban na fatan ganin an tsagaita bude wuta. Sai dai Majalisar ta Dinkin Duniya ta jaddada cewar tattaunawar ba ta kai tsaye ba ce.

Karin bayaniFatan tattaunawa don kawo karshen rikicin Sudan

 An dai kwashe sama da shekara guda ana gwabza fada a Sudan tsakanin sojoji da dakarun sa-kai, kuma rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 14,000 yayin da mutane 33,000 suka ji raunuka a cewar alkalumman Majalisar Dinkin Duniya. Kazalika kusan mutane miliyan 25  wato fiye da rabin al'ummar Sudan na bukatar taimako yayin da kusan mutane miliyan 18 na fuskantar matsalar karancin abinci.