1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masu sukar gwamnati na batan dabo a Kenya

December 28, 2024

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar Kenya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake garkuwa tare da batar da mutane da dama babu kakkautawa a fadin kasar.

Wani 'dan sandan kwantar da tarzoma a yayin arangama da matasa a Nairobi
Wani 'dan sandan kwantar da tarzoma a yayin arangama da matasa a Nairobi Hoto: TONY KARUMBA/AFP/Getty Images

Kungiyoyin sun ce tun daga lokacin da aka gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Yunin 2024, akalla an sace mutane 82, yayinda wasu mutanen 29 suka yi layar zana ko sama ko kasa.

Karin bayani: Amnesty na son a yi bincike kan murkushe boren matasa a Kenya

Kungiyoyin kare hakkin 'dan adam da dama ciki har da  Amnesty International da  Human Rights Watch sun zargi 'yan sanda da sauran jami'an tsaro wajen yin garkuwa da mutanen, zargin da 'yan sandan Kenyan ke ci gaba da musantawa. Ko a baya bayannan mutane uku da suka yi kaurin suna wajen caccakar gwamnatin Ruto sun yi batan dabo da suka hadar da Peter Muteti da  Billy Mwangi da kuma Bernard Kavuli.

Karin bayani: Matasan Kenya da kafar sada zumunta

Hukumomin kasar ta Kenya sun jinkinta gudanar da bincike kan dauki dai-dai da ake yi wa masu sukar manufofin gwamnatin Shugaba William Ruto a shafukan sada zumunta.