1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Masu yaki da makaman nukiliya sun lashe lambar yabo ta Nobel

October 11, 2024

An bai wa kungiyar mai suna Nihon Hidankyo lambar ce don kokarin da ta rika yi na hana amfani da makaman nukiliya.

'Ya'yan kungiyar Nihon Hidankyo
'Ya'yan kungiyar Nihon HidankyoHoto: KYODO/REUTERS

A ranar Juma'a ne a aka bai wa wata kungiyar da ke yaki da bazuwar makaman nukiliya mai suna  Nihon Hidankyo dake kasar Japan lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2024.

Kungiyar ta kunshi mutane da suka tsira daga harin bama-baman nukiliya da Amurka ta harba kan Hiroshima da Nagasaki.

Shugaban kwamitin na Nobel Jørgen Watne Frydnes ya ce an basu lambar yabon ce ta 2024 a yayin da haramcin amfani da makaman nukiliya ke fuskantar barazana.

Karin bayani:'Yan Amurka biyu sun lashe kyautar Nobel ta likitanci

Watne ya ce kwamitin na Nobel ya yanke shawarar karrama mutanen da suka tsira daga harin ne kuma suka ci gaba da yaki da amfani da makaman nukiliya duk da radadin da suka ji da kuma wahalhalu da suka fuskanta.

 

Karin bayani:An bayyana zakarun Nobel na bana

Shugaban kungiyar ta Hidankyo a yankin Hiroshima  Tomoyuki Mimak ya yi kwalla a yayin da aka sanar da sunan kungiyarsu a matsayin wacce ta samu lambar yabon ta 2024.