1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa sun sake fitowa a Kenya

June 20, 2024

Bayan alkawarin gwamnatin Kenya na duba yiwuwar rage tsadar haraji a kasar, dubban matasan kasar sun bijire tare da lasar takobin ci gaba da bore domin matsa wa gwamnati lamba domin ta yi gyara.

Masu zanga-zanga a Kenya
Masu zanga-zanga a kasar KenyaHoto: Kanyiri Wahito/ZUMAPRESS/picture alliance

Masu zanga-zanga a Kenya sun shirya sake dandazo a kan titunan fadin kasar, domin nuna turjiya ga kare-karen haraji da hukumomi ke ci gaba da yi, abin da suka yi amannar zai kara masu tsananin tsadar rayuwa.

Gwamnatin Shugaba William Ruto mai fama da karancin kudade dai ta amince a ranar Talatar da ta gabata cewa za ta dubi yiwuwar yin gyara-gyare ga harajin, bayan arangamar da ta wakana a tsakanin wasu daruruwan matasa da 'yan sanda a Nairobi babban birnin kasar.

Sai dai ga alamu gwamnatin ta Kenya, za ta ci gaba da wasu kare-kare a kan wasu haraje-haraje, a kokarinta na rage yawan basuka da take karbowa daga ketare domin matsalolin cikin gida.

Masu zanga-zangar a birnin Nairobi a yau, sun sha alwashin zuwa farfajeyar majalisar dokoki domin nuna fushinsu a kan yawan harajin da ake karba a kasar.