1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga shida sun mutu a Kenya

July 13, 2023

Mutane shida sun mutu yayin da wasu mutane da dama suka jikkata a wasu biranen kasar Kenya a yayin arangama da jami'an tsaro a lokacin da aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa ga gwamnati.

Hoto: THOMAS MUKOYA/REUTERS

Madugun adawan Kenya Raila Odinga ne ya kira zanga-zangar yana mai shan alwashin kifar da gwamnatin William Ruto wace ya kira da 'yar kama karya.

Tun da farko hukumomin kasar sun haramta yin zanga-zanga wace aka kira da nufin kalubalantar karin haraji kan ababen more rayuwa da kuma gazawar gwamnati wajen yaki da cin hanci.