1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga sun fantsama titunan Tel Aviv

July 7, 2024

Masu bore sun mamaye titinun birnin Tel Aviv domin mika bukata ga gwamnati ta cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas.

Masu zanga-zanga sun fantsama titunan birin Tel Aviv
Masu zanga-zanga sun fantsama titunan birin Tel AvivHoto: Ohad Zwigenberg/AP/picture alliance

A Isra'ila, masu zanga-zanaga sun mamaye hanyoyin birnin Tel Aviv domin mika bukata ga gwamnatin kasar da ta cimma yarjejeniyar sakin wadanda Hamas ke tsare da su, yayin da aka shiga wata na 10 da fara yakin Gaza.

Masu boren dauke da tutoci sun haifar da cunkuso a birnin, inda suke yin kira ga gwamnati da ta gudanar da zabe.

Tun da fari dai, jami'an 'yan sanda sun tsaurara matakan tsaro a kusa da gidan Firanminista Benjamin Netanyahu da ke birnin Kudus. Ko a ranar Asabar, sai da 'yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati da suka rufe manyan hanyoyi.

A yanzu haka masu shiga tsakani a yakin na Gaza sun kaddamar da sabuwar tattaunawa a tsakanin Isra'ila da Hamas, inda 'yan uwan wadanda ake tsare da su suka bayyana kyakyawan fata a kai.