Masu zanga-zanga sun fusata a Sudan
July 30, 2019Talla
Jagororin zanga-zangar sun ziyarci garin Al-Obeid da aka aikata kisan, ta'asar kuma da Majalisar Dinkin Duniya ta ce a yi gaggawar gudanar da bincike a kai.
A jiya Litinin ne aka kashe yaran 'yan makaranta a tsakiyar garin, kisan da masu adawa da gwamnatin suka ce na rashin imani ne.
Majalisar ta Duniya ta ce babu dalilin kashe dalibai cikin kayansu na makaranta haka kawai, tana mai cewa shekarunsu basu ma wuce 15 zuwa 17 da haihuwa ba.
Wasu ruwayoyi daga Sudan din, sun ma ce an bayar da shawarar garkame dukkanin makarantun da ke a yankin da wannan lamari ya faru.