1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Mata a Indiya na zanga-zanga kan halaka wata likita

August 17, 2024

Kisan gilla da aka yi wa matashiyar likitar ya sake aza ayar tambaya da kuma muhawara kan cin zarafin da ake yi wa ma'aikatan kiwon lafiya dama mata baki daya a kasar ta Indiya.

Likitoci da iyayen dalibai ke zanga-zanga a birnin Delhi don nuna fushinsu kan kisan wata likita
Likitoci da iyayen dalibai ke zanga-zanga a birnin Delhi don nuna fushinsu kan kisan wata likitaHoto: Manish Swarup/AP Photo/picture alliance

Dubban likitoci mata ne suka fantsama kan tituna a fadin kasar Indiya wajen gudanar da zanga-zanga, don nuna fushinsu kan kisan gillar da aka yiwa wata matashiyar likita a wani asibiti da ke gabashin kasar a jihar Arewacin Bengal.

Karin bayani: Zanga-zangar dokar zama dan kasa a Indiya

An dai samu gawar matashiyar likitar 'yan shekaru 31 a kwalejin asibitin RG Kar da ke Kolkata. Binciken kwakkwafin da aka yi wa gawar an gano munanan raunuka a jikinta da ke alamta cewa an ci zarafinta kafin daga bisani a halaka ta.

Karin bayani: Masu zanga zanga sun mutu a Indiya 

Firaiministan Indiya Narendra Modi, ya nuna takaicinsa kan yadda ake cin zarafin mata a kasar, a wani jawabi da ya gabatar kan cikar kasar shekaru 78 da samun 'yancin kai, Modi ya ce ya damu matuka kan yadda ake gudanar da mummunar ta'addanci akan iyaye mata.

Tuni dai hukumomin yankin suka cafke wani 'dan sandan sa-kai da ake zargi da hannu a kisan matashiyar likitar. Kungiyar Likitoci ta kasar ta Indiya ta ce kaso 75% bisa dari na ma'aikatan lafiya sun taba fuskantar cin zarafi a tarihin aikinsu.