Mata da dama sun samu mukamai a Kenya
August 31, 2022‘Yan gwagwarmayar neman cike gibi da ke tsakanin maza da mata ta fuskar shugabanci a Kenya, sun bayyana samun karuwar mata a mukaman siyasar kasar da cewa wani babban ci gaba ne aka samu. Wannan yabon ya biyo bayan samun karuwar mata a majalisun kasar, inda aka samu mata uku da suka ci mukaman Sanata da kuma sama da 33 da suka samu a majalisar wakilai.
Ga misali a fitaccen yankin nan na Nakuru, mata takwas suka samu mukami da suka hada da na gwamna da kuma sanatoci. Susan Kihika ta lashe mukamin gwamna a gundumar Nakuru tare da yaba wa masu zabe da suka ga dacewarta a wannan mukami.
Gwamna Kihika ta ce: " Ga wadanda suka zabe ni da ma wadanda ba su yi ba, godiya nake yi da gani da kuka yi da dacewata da wannan mukamin. Na zama gwamna ta uku kuma mace ta farko da za ta jagoranci al'amura na wasu shekaru biyar. Zan kasance gwamnar kowa ba tare da bambanci ba."
Mata da dana sun samu nasara a zaben 'yan majalisar Kenya
Kasar Kenya ta dauki lokaci na ganin mata sun shiga sahun jagoranci ta yadda za su kara da mazan da suka mamaye mukamai. Susan Kihika, ta yi imanin cewa mata za su taka rawar da ba a yi zato ba. Ta ce: " Na tabbatar wa kaina cewa dole ne in yi aiki tukuru domin mace ce ni. Abin takaici ne wannan tunani na rauni da aka dora wa mata. Ba na jin dadin gani da jin haka, domin ko da an samu namiji da gazawa, ba ya zama labari amma mata a ci gaba da yamadidi da mu. Wannan kalubale ne da nake ganin zan fuskance shi."
Matashiya Linet Chepkorir mai shekaru 24, guda daga cikin ‘yan majalisar wakilai da aka zaba a gundumar Bomet a Kenya, t a ce ya kamata nasarar da ta samu ta zaburar da matasa mata domin shigowa fagen siyasa saboda su maida hankali wajen maganin matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.
Chepkorir ta ce: " A tsarin rayuwata na tashi da jagoranci ne tun daga gida zuwa makaranta, kai har ma a coci ina rike mukamai. Ina son gabatar da kudurin da zai taimaka wa ‘yan matanmu da sauran mata. Kamar yadda ake samar da litattafai kyauta a makarantu, ina son a rika samar da kayan tsaftar mata ta al'ada a kyauta su ma. "
An mutunta kaso mata a matakan takara a zaben 2022
A zabuka shida ne dai ‘yan kasar Kenya suka kada kuri'u, kama daga na shugaban kasa da na wakilan kasa da gwamnoni da sauran mukamai da dama a farkon wata na Agustan 2022. Kamar kuma yadda yake cikin kundin tsarin mulkin kasar, babu jinsin da ya kamata ya wuce biyu bisa uku na mukaman siyasa da ake da su a siyasance a Kenya.