Mata masu wakokin zaman lafiya a Sudan
September 7, 2016Kasar Sudan dai ta yi kaurin suna a kafofin watsa labaran kasa da kasa, wajen yawan rikice-rikice, to amma Allah ya albarkaci kasar da tarin baiwar mawaka da al'adun gargajiya masu kayatarwa. Lamarin da ya san'ya wata kungiyar mawaka ta mata zalla a kasar, ta tashi haikan don ganin ta canja irin wannan mummunan kallon da akewa kasar ta Sudan.
Kungiyar ta mata zalla mai suna "Salute Yal Bannot"wato "Ku mu girmama mata" da ta kunshi mata da 'yan mata 11, da ke zama irinta ta farko a kasar tun bayan fara aiwatar da tsarin shari,a a kasar a shekarun 1980, kungiya ce da ke gabatar da wakokinta cikin harsunan Larabci da Turancin Ingilishi, da zimmar sauya irin kallon da duniya ke wa kasar ta Sudan, ta hanyar bayyana irin rawar da mata ke takawa a bangarorin siyasa da zamantakewa a wake wakensu, yunkurin da kungiyar ta ce tana yinsa ne don dinke barakar da rikice-rikicen kabilanci da na addini suka haifar a kasar, a ta bakin daya daga cikin wadannan 'yan mata mai suna Saraah:
"Muna fata mutane na sauraronmu a ko ina. Burinmu mu ga sauyi ya wanzu a kasarmu. Ba muna waka don nishadantarwa kadai ba ne. Muradinmu mu ga an samu sauyin da zamu iya ganinsa a kasa."
Rikice-rikicen kabilanci da na siyasa gami da na addini a kasar ta Sudan dai sun kai ga dara kasar biyu shekaru shidan da suka gabata, yadda kudancin kasar na galibin kiristoci ya kafa kasarsa ta Sudan ta kudu mai cin gashin kanta, amma duk da hakan, ba a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a sabuwar kasar ta Sudan ta kudun ba. lamarin da ya sanya mawakan na "Salute Yal Bannot" ke nuna irin rawar da ya kamata mata su taka wajen magance irin wadannan matsaloli a kasar, a ta bakin Heeba daya daga cikin mawakan:
"Na yi amanar cewa, ganin gungun mawaka mata kan dandamali suna rera waka kan zaman lafiya a Sudan zai yi matukar yin tasiri a zukatan masu sauraro. Muna son karawa mata karfin gwiwar fitowa su bayyana albarkacin bakinsu ba da tsoro ko fargaba ba."
Ko da yake su kansu wadannan mawaka suna fuskantar musgunawa a wasu lokutan daga dangi ko al'umma, amma, a ta bakin Yasmeen, daya daga cikin mawakan, hakan ba zai sanya su yin kasa a gwiwa a fafutukar da suke yi ba:
"Idan ke mawakiya ce, za ki dinga burge mutane saboda nishadantarwar da kike musu, amma da zarar an zo batun kimantawa ko mutuntawa sai ki ga ana miki ganin ganga ba rufi. Mutane na kyamar yin aure ko hulda da kai, don ba sa ganinka da mutunci."
A yanzu haka dai, mawakan na "Salute Yal Bannoot", sun dukufa wajen rera wakokinsu da ke bayyana irin gwagwarmayar da matan Sudan ke yi, tare da rera wakokin soyayya da yin riko da kyawawan al'adu da zaman lafiya.