Amnesty ta zargi Sojojin Najeriya da lalata
May 24, 2018Talla
Kungiyar ta ce ta samu shedu kan zargin da ke nuna dakarun na amfani da matan kamin basu abinci, Amnesty ta koka kan rashin daukar kwararan matakan hukunta wadan da ake zargi duk da tarin hujjoji da ke gaban hukumomi.Tun shekarar 2016 'yan sanda ke kokarin bankado irin ta'asar lalata da ake zargin sojojin na aikatawa a sansanonin 'yan gudun hijira, amma sojojin sun sha musanta zargin.Kungiyar Amnesty International a Najeriya, ta ce lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari zai cika alkawarin kare hakkin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.