1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Mata na iya mallakar filaye a Saliyo

February 1, 2024

A kusan dukkannin nahiyar Afirka maza su ke iko da filaye, in ban da wadanda kamfanonin kasashen waje suka mallaka ba tare da mazan sun ankara ba.

Hoto: Jane Hahn/AP/picture alliance

 A yunkurinta na sauya wannan lamari, kasar Saliyo ta amince da wasu sababbin dokoki biyu wadanda za su bai wa mata damar mallakar filaye da kuma sayar da su ga kamfanonin kasashen waje idan suna bukata. Salihu Adamu Usman ya duba mana wannan batu.

Wadannan sababbin dokoki, na da matukar muhimmanci ga matan kauyen Tonkolili na Saliyo. Susan Konteh ma'aikaciyar wata kungiya ce mai zaman kanta ta Land Rights da ke taimakawa mutane sanin dokoki kan mallakar filaye. Burinta shi ne taimaka wa mata su karbe iko da filayensu idan mazajensu sun rasu, ko da yake ba wannan ne kadai abin da kungiyar ke yi ba. Kuma ita ce ta sanar da matan sababbin dokoki da suka jibanci mallakar filayensu, tare da karfafa musu gwiwa wajen kato hakkokinsu.

 

Konte kenan take cewa "Filina rayuwata, na zo ne domin in karafafa muku gwiwowinku in kuma shaida muku gwagwarmayar da na yi a matsyina na mace domin ku yi kokarin kwato hakkokinku.  filayenku ne rayuwarku ce kuma hakkinku ne".

A shekarar da ta gabata, Saliyo ta amince da dokoki masu yawa da ba kasafai ake ganin irnsu ba a nahiyar Afrika. A karon farko mata na da iko su mallaki filaye tare da zabar abin da suke so su yi da filayen ba tare da katsalandan daga maza ba.

Edna Bangura na da filaye a kasar ga kuma abin da take cewa:

"Ina da filaye a nan da can, kusan a baki dayan kauyenmu. Sun zagaye kauyen gaba daya, na fi kowa filaye a kauyen nan a matsayina na mace."

Alokacin da mijin Bangaura ya rasu, al'ummar kauyen sun kwace filayensa daga garet,a sai ta kai su kotu kuma ta yi nasara.

"Na tsaya kan kafafuna sosai, babu wanda ya isa ya kwace min wannan filin nawa. Hakan ba zai taba faruwa ba. Daga gonata na tsinko wannan lemon da safiyar nan, yana da alfanu sosai. Saboda na kwato filina daga mugayen mutane."

Amma fa ba al'ummar gari ne kadai ke kwace iko da filayen mata idan mazajensu suka mutu ba. Misali shi ne abin da ya faru da Susan Konteh, domin kuwa bayan rasuwar mijinta, danginsa sun sayarwa da wani kamfanin Chaina filayensa amma sabuwar dokar ta taimaka mata wajen sake kwato filayen. Tun a lokacin take ta fafutukar ganin sauran mata ba su fada irin halin da ta shiga ba.

Masana shari'a dai na ganin wadannan dokokin na mallakar filaye ga mata za su yi tasiri, to amma dai duk da haka ana bukatar tashi tsaye kamar yadda Susan ta yi domin bai wa mata bila'adadin a Saliyo damar mallakar filayensu