Mata na neman 'yancin zubar da ciki a Amirka
October 2, 2021Daruruwan mata masu fafutikar neman halalta zubar da ciki a Amirka sun mamaye titunan manyan biranen kasar a ranar Asabar, inda suke bukatar hukumomi su yi watsi da al'adar nan ta hana mata 'yancin iya barar da abin da ke a cikinsu.
Matan na Amirka na kara matsin lamba a kan batun zubar da cikin ne, bayan amincewa da haramcin zubar da ciki, da jihar Texas ta yi a ranar daya ga watan Satumba.
Yayin da ake kwanaki biyu kafin kotun kolin Amirka ta yanke hukuncin karshe a kan batun ne, kungiyoyin mata kimanin 200 ke wannan gangami na nuna bukatar gwamnatin kasa ta ba su dama ko 'yanci a kan zubar da cikin.
Matan za su karkare ne da wani gagarumin gangamin da za su yi a birnin Washington, inda dubbai daga cikin su za su hallara a harabar kotun kolin kasar, domin neman sake dawo da 'yancin mata na yin hakan bayan shekaru 50.