1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata sun ja damarar neman mukamai a Najeriya

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
September 22, 2025

Kungiyoyi mata sun yi maci a Najeriya domin gabatar da bukatarsu ta neman karin kujerun da za su yi takara don samun mukamai a siyasar Najeriya da suke koke an bar su a baya sosai.

Wasu mata 'yan gwagwarmaya a Najeriya
Wasu mata 'yan gwagwarmaya a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Dubban kungiyoyi mata ne suka yi maci a Abuja domin gabatar da bukatarsu ta neman karin kujerun da za su yi takara don samun mukamai a siyasar Najeriya da suke koke an bar su a baya sosai. Suna wannan ne a dai dai lokacin da ake zaman jin ra'ayin jama'a a kan gyare-gyaren da za a yi wa kundin tsarin mulkin Najeriyar.

Kungiyoyin matana ne suka yi tattaki suna rera wakoki a Abuja domin gabatar da wannan bukata tasu saboda koma bayan da suke fuskanta a siyasar kasar. Domin duk da yawan da suke da shi da jurewa wajen yin zabe har yanzu matan Najeriya na a baya inda cikin adadin 'yan majalisar dattawa 109 guda 4 ne kacal mata, a majalisar wakilai ma mata 17 ne kadai daga cikin 'yan majalisar wakilan su 360 da ake da su. 

Mata 'yan jarida masu gwagwarmaya a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Duk da rajin da suke yi a Najeriyar, akwai sama da jihohi 14 da babu mace da ke rike da ko da mukami guda na siyasa, abin da ke nuna koma baya, shekaru 30 bayan taron mata da aka yi a Beijing.

Akwai dai mata masu bukata ta musamman da suka goya wa matan baya, a ciki kuma har da mutane masu bukatar ta musamman.

Sassan tsarin mulkin Najeriya 89 ne ake son yi wa gyaran fuska da suka hada da sauya ikon bai wa shugaban Najeriya damar nada shugaban hukumar zabe da bai wa kananan hukumomin 'yancin cin gashin kansu da bai wa jihohi ikon arzikin da suke da su, da batun kafa 'yan sandan jihohi. Duka wadanan sai an samu amincewar jihohi 24 kafin su zama doka, abin kuma da ke nuna da sauran aiki da ke a gaba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani