Cote d'Ivoire: Mata na da tasiri a zabe?
September 25, 2025
'Yan takarar shugaban kasar Cote d'Ivoire Simone Ehivet Gbagbo da Henriette Lagou Adjoua dai, yanzu haka na aiki tukuru kan dabarun da za su tinkari 'yan kasar da su gabanin bude yakin neman zabe a ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa.
Simone Ehivet Gbagbo shugabar jam'iyyar MGC da Henriette Lagou Adjoua shugabar jam'iyyar RPC, su ne fitattun mata 'yan siyasa da za su kasance kallabi cikin rawuna a zaben.
Karin Bayani:Tsofaffi sun mamye siyasar Afirka
Takarar wadannan matan biyu wani gagarumin ci-gaba ne ga kokarin damawa da mata a fagen siyasar Cote d'Ivoire, inda tsawon shekaru maza suka yi kaka-gida.
Rawar da mata za su taka
A cikin tsare-tsarenta na samun goyon bayan 'yan Cote d'Ivoire, 'yar takara Simone Gbagbo ta bayar da fifiko kan hadin kan al'ummar kasar da a shekarun baya ta yi fama da babban rikicin siyasa: "Babban abun da zan ba fifiko shi ne kaddamar da tattaunawa a tsakanin al'ummar Cote d'Ivoire, saboda abu ne da ke ciwa da dama tuwo a kwarya....." A cewar Simone Gbagbo.
Ita dai Simone Gbagbo ta kasance uwargidan tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurant Gbagbo daga shekarar 2000 zuwa 2011, sannan kuma tarihi ya shaida karfin fada a ji da take da shi a fagen siyasar kasar. Hakazalika ta yi gwagwarmaya a kungiyoyin kwadago da na siyasa da dama, kafin ta zama mataimakiyar shugaban majalisar dokoki kuma mai bai wa tsohon mai gidanta shawara a lokacin mulkinsa.
Karin Bayani:Kotu ta yanke wa Simone Gbagbo hukuncin ɗaurin shekaru 20
Sai dai Simone Gbagbo da ake wa lakabi da 'Mace mai lakalmin karfe' ta taba fadawa komar kotu, inda aka yanke mata hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso saboda rawar da taka a ricikin siyasar da ya biyo bayan zaben 2010 zuwa 2011 kafin a yi mata afuwa a shekarar 2018.
Ita kuwa Henriette Lagou Adjoua ta kasance ministar kula da harkokin mata ta Cote d'Ivoire, karkashin mulkin tsohon shugaban kasar Laurant Gbagbo. Kuma wannan na zama karo na biyu da ta ke tsayawa takarar neman mukamin shugaban kasa.
Fatan samun goyon baya
Sai dai a wannan karo 'yar siyasar mai shekaru 66 a duniya ta tsaya takarar ne a karkashin inuwar hadakar jam'iyyu masu fafutukar zaman lafiya da ake wa lakabi da GP Paix, kuma a fadarta: "Tsarinta ya ta'allaka ne a kan mata takwarorinta."
Wadannan 'yan takara dai Simone Gbagbo da Henriette Lagou Adjoua na saka ran samun kuri'un magoya bayan Laurant Gbagbo da na Pascal Affi N'Guessan da kuma naTidjane Thiam da aka yi watsi da takardunsu, har ma da fatan samun kuri'un wadanda suka yi wa jam'iyyar ShugabaAlassane Ouattara tawaye.
Matan biyu sun kuma dau alwashin taka rawar gani a fagen siyasar Cote d'Ivoire, domin a mahangarsu dimukuradiyya ta gaza a kasar saboda rashin damawa da mata.