1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mataimaki na hudu ya jagoranci zaman majalisar dokokin Nijar

Gazzali Abdu TasawaOctober 1, 2014

'Yan majalisa daga bangaren Hama Amadou sun kaurace wa taron majalisar kan kasafin kudin kasar ta Nijar saboda a cewar su zaman ya sabawa doka.

Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Hoto: DWM. Kanta

Zaman taron majalissar dokokin kasar wanda a karo na farko a cikin mulkin jamhuriya ta 7 ya wakana ba a karkashin jagorancin shugaban majalissar dokokin kasar Malam Hama Amadou ba, wanda ya gudu daga kasar yau sama da wata daya.

Kasancewa mataimakin shugaban majalissar dokokin na farko ya tafi aikin hajji kuma mataimaka na biyu da na uku wadanda 'yan adawa ne na bijirewa guraban na su a kwamitin gudanarwar majalissar, ta sanya a karo na farko mataimaki na hudu na shugaban majalissar dokokin kasar Honnorable Ben Omar Mohamed ne ya jagoranci bikin bude taron majalissar, kuma Jim kadan bayan bude zaman taron ya bayyan gamsuwarsa da ma ra'ayinsa a kan matakin da wasu 'yan majalisar dokokin adawa suka dauka na kaurace wa zaman taron.

A jawabin bude zaman taron na sa shugaban ruko na majalissar dokokin kasar ta Niger Ben Omar Mohamed ya ambato jerin kalubalan da ke a gaban kasar ta Niger musamman a fannin tsaro da kiwon lafiya da ilimi da dai sauransu da ma kuma irin kokarin da gwamnatin kasar ta ke yi tare da goyan bayan kasashen duniya na shawo kansu. Dokoki da dama dai majalissar za ta yi nazari akan su musamman dokar kasasfin kudin kasa ta shekara mai kamawa ta 2015.

Bikin bude zaman taron majalissar na yau wanda 'yan majalissar dokoki
na jamiyyun adawa suka kauracewa ya samu halartar jakadan kasashen waje
na Amurka da turai da ma na wasu kasashen Afrika aminan kasar ta Niger da ma kuma 'yan majalissar dokoki na jamiyyun adawa ma su da'awar goyan bayan gwamnati.

Hoto: Mahaman Kanta