1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus ya kai ziyara Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 25, 2025

Lars Klingbeil wanda shi ne ministan kudin Jamus, yana aiki kafada-da-kafada da shugaban gwamnati Friedrich Merz kan Ukraine

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Lars Klingbeil, lokacin da ya sauka a Ukraine da safiyar Litinin 25.08.2025
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Da safiyar wannan Litinin mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Lars Klingbeil ya sauka a birnin Kiev na kasar Ukraine, domin tattaunawa da mahukuntan kasar, kan gudunmawar da Jamus za ta bayar don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Mr Klingbeil, wanda shi ne ministan kudin Jamus, ya ce yana aiki ne kafada-da-kafada da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz kan wannan kuduri da suka sa a gaba, na ganin sun ba ta kariya, tare ma da samar da ingantaccen tsaro na nahiyar Turai.

Baya ga mahukuntan Ukraine da zai gana da su, haka zalika Klingbeil zai taba alli da 'yan majalisar dokokin kasar da kungiyoyin rajin kare hakkin al'umma, tare da tuntubar kawayen Jamus na duniya, a kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na bayar da kariya ga Turai.

karin bayani:Ko Trump zai kalubalanci Rasha a kan Ukraine?

A baya bayan ne shugaba Donald Trump na Amurka ya karbi bakuncin shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, tare da tawagar shugabannin Turai, inda suka tattauna kan hanyoyin bi don kawo karshen yakin Ukraine da Rasha.