1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Mataimakin shugaban Iran ya janye daga takarar shugaban kasa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 27, 2024

Mr Hashemi mai shekaru 53, na daya daga cikin mataimakan shugaban kasa marigayi Ebrahim Raisi

Hoto: Iranian State TV/ZUMA/picture alliance

'Daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a Iran mai suna , ya janye daga shiga zaben da za a yi na maye gurbin tsohon shugaban kasar marigayi Ebrahim Raisi, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Karin bayani:Amirhossein Ghazizadeh Hashemi

Mr Hashemi mai shekaru 53, na daya daga cikin mataimakan shugaban kasa marigayi Ebrahim Raisi, kuma ya taba tsayawa takarar shugabancin Iran a shekarar 2021.

Karin bayani:Iran ta kore shakku kan kashe Shugaba Raisi aka yi

Yanzu haka dai 'yan takara 5 ne suka rage, a yayin da ake shirin gudanar da zaben ranar Juma'a.