SiyasaArewacin Amurka
Mataimakiyar firaministar Kanada ta ajiye aiki
December 17, 2024Talla
Mataimakiyar Firaministar Kanada kana ministar kudi, Chrystia Freeland ta yi murabus daga bakin aiki kuma tana cikin manyan ministocin gwamnatin Firaminista Justin Trudeau. Wannan matakin ya janyo tambayoyi game da matsayin firaministan.
Karin Bayani: Justin Trudeau zai yi wa'adi na uku
Tuni masu adawa na bangaren masu ra'ayin mazan jiya suka nuna irin radanin da gwamnatin kasar ta Kanada ta shiga, na samun sabani tsakanin mambobin jam'iyya mai mulki.