Matakan inganta harkar hada fina-finan Hausa
November 14, 2017A karon farko, gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta shirya wa masu fina-finan Hausa bita ta musamman, ta yadda fina-finan da suke shiryawa za su dace da bukatun al’uma; da kuma yin gyara ga irin kura-kuran da ake samu. Matasa masu fina-finan a wannan masana’anta na fannoni daban-daban ne gwamnatin Kanon ke baiwa horon domin sun kaiga shirya fina-finai masu ma’ana da za su karbu ga jama’a.
An dai jima ana jan hankalin masu shirya fina-finan Hausa a Najeriya dangane da fitowa da wasu abubuwan da bas a dacewa da bukatun al’uma masu kallo, wanda ginshiki ne babba da ya sa ake gudanar da horon. Shigowar gwamnati da nufin yin gyara ga irin kura-kuran da masu fina-finan ke yi, zai kawo ci gaba da ake so.
Baya ma ga batun kura-kurai, akwai kuma batun rashin kayan aiki na zamani da ke shafar ingancin harkar ta fina-finan Hausa a Najeriya. Mahalarta bitar dai, sun bayyana farin ciki da abubuwan da suka amfana da su a fannonin duka, da suka hada da gyaran kura-kuran da kuma karuwar. Horon, ya hada ne da batun nakaltar yin fim a rubuce da kuma na fita don gabatar da shi a aikace da zimmar samar da gajerun fina-finan na gwaji, domin auna fahimtar kowane daya daga cikinsu.