1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jamus ta dawo da matakan tsare kan iyaka

September 16, 2024

Cunkoson masu neman mafaka, ya sanya ministar harkokin cikin gida ta Jamus daukar matakin fara gudanar da bincike a kan iyakokin kasar. Wannan matakin dai, na nufin dakile kwararar bakin haure cikin kasar.

Grenze Belgien Deutschland | Grenzkonotrollen anlässlich der UEFA EURO 2024
Hoto: Christoph Hardt/Panama Pictures/IMAGO

Mataki ne dai da a kan iya dauka a karkshin dokokin kula da bakin haure na kungiyar Tarayyar Turai EU, idan bukatar hakan ta taso. Daga wannan Litinin din 'yan sandan Jamus sun fara gudanar da binciken takardun masu shiga kasar a kan iyakokinta baki daya, ba wai kawai a iyakokin gabashi da kudanci da a baya suke gudanar da binciken ba. Za a ci gaba da gudanar da binciken har zuwa watanni shidan da ke tafe a kan iyakokin arewaci da yammaci da suma za su bi sahu. Wannan bincike dai, zai shafi masu shiga Jamus ta kan iyakokin kasar da kasashen Denmark da Holland da Beljiyam da Luxembourg da kuma Faransa. Ministar harkokin cikin gida ta Jamus Nancy Faeser ta bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne sakamakon yawaitar shigar bakin haure kasar ba bisa ka'ida ba. Jamus dai na tsakiyar kasashen kungiyar Tarayyar Turai da ake iya shiga da takardar izinin shiga kasa ta Schengen, wadda ta hada kasashen Turai 29.

Karin Bayani: Scholz: Za mu tsaurara doka kan hari da wuka

Wadannan kasashe sun sahale binciken takardun masu shige da fice a tsakaninsu, inda ake bukatar fasfo daga filayen jiragen sama na kasashen kadai. Ana dai ganin sabon tsarin gudanar da binciken a kan iyakoki da Jamus ta fito da shi, ka iya janyo tangarda dangane da zirga-zirgar mutane da ma kayan masarufi. Ba dai Jamus ce kadai kasar da ta dauki matakin tsaurara binciken masu shige da fice a kan iyakokinta ta kasa ba, akwai karin kasashe takwas da ke karkashin tsarin na Schengen da suma  suka dauki makamancin matakin na Berlin. Tun daga shekara ta 2006 kawo yanzu an samu rahoton binciken kwakwaf har 441, a kan iyakokin kasashen da ke karkashin tsarin na Schengen kuma Faransa ce ke kan gaba. Tuni ma dai firaministan Poland Donald Tusk ya soki matakin na Berlin, yana mai cewa zai janyo barazana ga tsarin takardar izinin shiga kasashen ta bai daya wato Schengen.

Nema da samun mafaka a kasar Jamus

04:32

This browser does not support the video element.

Haka nan ma kungiyar Ma'aikata ta 'Yan Sandan Jamus din da kanta, ta yi korafin cewa ba su da adadin 'yan sandan da ake bukata wajen gudanar da bincike a koda yaushe a kan iyakokin kasar. A cewarta a yanzu haka ma mambobinta na yin aiki fiye da yadda ya kamata su yi, inda ake bukatar karin jami'an 'yan sanda 5,000 domin su gudanar da wannan aiki. Sai dai Hukumar 'Yan Sandan kasar ba ta amince a ikirarin kungiyar ma'aikatan ba, inda ma'aikatar cikin gidan Jamus din ta ce akwai wadatattun jami'ai da za su gudanar da aikin. A cewar rundunar 'yan sandan Jamus, kimanin mutane dubu 34 ne suka yi kokarin shiga kasar ba tare da izini ba tsakanin watan Janairu zuwa Yulin wannan shekara da muke ciki. Daga cikinsu an hana kimanin dubu 17 shiga tun daga kan iyakokin kasar, yayin da aka kyale sauran suka shiga ake kuma kula da su karkashin dokokin rarraba 'yan gudun hijira na kungiyar Tarayyar Turai da ake wa lakabi da Dublin Regulation.

Karin Bayani: 'Yan Afghanistan sun samu mafaka a Jamus

A shekarar da ta gabata ma rundunar 'yan sandan Jamus din ta cafke mutane dubu 127 a kan iyakar kasar yayin da suke kokarin shiga ba tare da izini ba, inda aka hana daya bisa uku na wannan adadi damar shiga. Ministar harkokin cikin gidan ta Jamus Nancy Faeser na son amfani da wannan sabon matakin bincike na kan iyaka, domin hana shiga kasar ba bisa ka'ida ba. Sai dai za a iya hana su shiga Jamus din ne kawai, idan ba su mika takardunsu na neman mafaka ba. Amma in har a kan iyakar suka nemi mafakar, mahukuntan Jamus na iya bincike su ga ko sun cancanta ko kuma sun nemi mafaka a wata kasar ta EU. Faeser na bukatar a gaggauta sake tattauna wa kan matsayar daukar nauyin masu neman mafaka a kasashen EU, tare da zama kan tebur da sauran kasashe mambobin kungiyar domin samun matsaya. A yanzu Hungary ce ke shugabantar Hukumar Tarayyar Turai, kuma gwamnatin kasar ta yi kakkausar suka a kan wannan sabon mataki da Jamus ta dauka cikin wata sanarwa da kakakinta ya fitar. Tsawon shekaru Hungary na shan suka dangane da daukar tsauraran matakai a kan 'yan gudun hijira, amma a yanzu tana sukar matakan da Jamus ke dauka.