Najeriya: Matakan kariya daga cutar sankara
November 27, 2024Horon na tsawon kwanaki biyu da Cibiyar Bincike a kan Cututtukan Sankara ko Cancer da Magancesu wato National Institute for Cancer Research and Treatment da hadin guiwar ma'aikatar lafiya ta jihar Sakkwato suka shirya, na da nasaba ne ga karuwar ciwon hanta da ake samu a cikin al'umma. Manufar shirya horon ga jami'an lafiya a matakin na farko da na biyu ita ce, domin su rika iya ganowa tare da tantance nau'o'i da alamomin cutar cikin sauki. Ma'aikatar lafiya ta jihar Sakkwato ta yi nuni ga irin yadda ake samun karuwar ciwon hanta musamman nau'in B da C, kuma sun yi amannar ta irin wadannan hanyoyi na horo da wayar da kai ga jami'an lafiya kadai ne za a iya magance ta. An dai zakulo jami'an lafiya daga asibitoci dabam-dabam na jihar Sakkwaton, domin su amfana da horon su kuma kara samun ilimi kan yadda za su gano ciwon hantar. Alkaluman Hukumar Lafiya ta duniya WHO na shekara ta 2023 da ta gabata, sun nuna 'yan Najeriya miliyan 20 ne ke dauke da ciwon hanta nau'in B da C. Wannan ya sanya kara kaimi wajen wayar da kai a kan muhimmancin gwajin cutar, musamman lokutan aure.