Kariya daga cutuka da ke da alaka da nunfashi
December 27, 2019Talla
Kashi biyu daga cikin ukun fadin kasar Nijar dai hamada ce, hakan ya sanya al'ummarta cikin barazanar kamuwa da wasu cututtuka da ke da nasaba da yanayi na sanyin hamatan.
Likitoci da kwararru a fannin kula da lafiya dai kan yi gargadi ga al'umma na kiyayewa a irin wadannan lokuta masu tsanatar yanayi. Tuni dai jama'a suka fara daukar matakai na kariya
Masu larurar rashin lafiya kamar Asma da Nimoniya kan kasance cikin mawuyacin hali. Amma rashin lafiyar da ta fi yawa tsakanin jama'a da kuma yaduwa musamman tsakanin yara kanana da tsoffi dai ita ce mura.
Yanayin wannan majinar da dan banbanci da wanda aka saba gani, kuma idan ba mataki aka dauka ba, zata rikide zuwa cutar da ke taba numfashi har ta kai ga huhu watau nimoniya