Matakan tsaro a Slovakia gabanin taron EU
August 12, 2016Talla
Ivan Netik da ke magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida ya bayyana cewa an tsaurara matakan tsaron ne a filayen tashi da saukar jiragen sama na Bratislava da Poprad da Kosice.
Kungiyar ta EU dai ta tsara babban taron kolinta za a yi a birnin Bratislava da ke zama babban birnin kasar ta Slovakia a ranar 16 ga watan Satimba inda za a tattauna kan makomar kungiyar bayan da Birtaniya ta zabi ficewa a watan Yuni.