An binne Mugabe a mahaifarsa
September 28, 2019Talla
An tsara gudanar bankwana da ya kunshi 'yan uwansa da gayyatattun abokai, bayan kai ruwa rana na makonni da gwamnatin da ta tilasta Mugabe sauka daga mulki, dangane da inda za a binne tsohon jagoran da ya yi fafutukar samar wa da Zimbabuwe 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Baki da aka tantance ne kadai ke halartar jana'izar mutumin da akasarin al'ummarsa ke masa kallon "Gwarzon shugaba". Mai magana da yawun jam'iyyarsa ta ZANU-PF Simon Khaya Moyo ya bayyana rashin dacewar tsarin yi wa Mugabe bankwana ta karshen.