Matakan tsuke bakin aljihu a Girka na fuskantar fushin al'umma
October 19, 2011Tun farkon shekara da mu ke ciki ƙasar Girka ta shiga kanun labarun Duniya, dalili da matsananciyar karayar tattatalin aziki da ta abka mata. Ƙungiyar ƙasashe masu amfani da takardar kuɗi ta Euro ta ɗauki matakai domin ceton Girka daga wanan mummunan hali. To sai dai a wani abu mai kama da ana magani kai kaba, ƙasar sai kara fadawa tace cikin matsalolin kuɗi.
A farkon watan da mu ke ciki shugabanin ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai su ka cimma daidaito domin kara taimakawa ƙasar da tsabar kuɗi euro miliyan takwas, amma a sharaɗin hukumomin birnin Athens su kara ɗaukar matakan tsimi da tanadi, abin da ƙungiyoyin kwadagon ƙasar suka ce ba za ta saɓu ba, wai bindiga a ruwa.
A tarayyar Nigeria kuwa a jiya ne aka gudanar da taron ƙasa dangane da tsara hanyoyin inganta tattalin arziki a Dutsen jihar jigawa. Don jin yadda masharahantan ke fassara tattalin arzikin Najeriya Halima Balaraba Abbas ta tuntuɓi Dr Suleiman Magaji na sashin ilimin tattalin arziki a jamiar Abuja don jin ko da wane ido yake kallon tattalin arzikin Najeriya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita : Zainab Mohammed Abubakar