1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu: Matakan yaki da cin-hanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 15, 2023

Kasa da wata guda da darewarsa kan karagar mulkin Najeriya, sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya fara farautar wadanda ake zargi da almundahana a kasar.

Najeriya | Naira | Cin-hanci
Matakan yakar cin-hanci a NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Duk da cewa har zuwa wannan lokaci bai kafa majalisar ta zartaswa ba, amma shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mayar da hankali a kan wannan matsala da ta zama dalili na koma bayan tattalin arziki da ma zamantakewar alumma.

Tun da fari dai, sabon shugaban na Najeriya ya bayar da umurnin dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele kafin daga bisani jami'an tsaron farin kaya su yi awon gaba da shi tare da tsare shi a komarsu. Ana dai zargin Emifiele da hannu a almundahana da kudin al'ummar Najeriyar, baya ga wasu jerin zarge-zarge da ake masa.

Bayan tsohon gwamnann babban bankin Najeriyar dai, Shugaba Tinubu ya bayar da umurnin dakatar da shugaban Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta Najeriyar EFCC Abdulrasheed Bawa. Bayan dakatar da shi din ne kuma, shi ma ya bi sawun Emefiele zuwa komar Hukumar Tsaron ta Farin Kaya da kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna