1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Yaki da sabon nau'in Covid-19 a Afirka ta Kudu

Adrian Kriesch Fauziyyah Dauda) (SB
December 10, 2021

Yayin da ake karfafa matakan yaki da Omicron wadda ke zama sabon nau'in cutar Covid-19 a Afirka ta Kudu, an zabi magajin garin mace bakar fata ta farko a birnin Johanneburg wadda kwararriyar likita.

Südafrika | Mpho Phalatse in Johannesburg
Hoto: Adrian Kriesch/DW

A Kasar Afirka ta Kudu, an zabi magajin garin mace bakar fata ta farko a birnin Johanneburg; kwararriyar likita da ake ganin akwai jan aiki a gabanta yayin da kasar ke fuskantar barazanar annobar cutar Corona karo na hudu bayan bullar sabon nau'in cutar na Omicron.

A birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, akan gudanar da tarukan liyafa a yammacin kowace rana, mutane kan taru ba tare da sun mutunta dokokin corona na sanya takunkumi da kuma ba da tazara tsakanin juna ba. Hakan ta sanya shugabanni ke cigaba da nuna dan ratsa ga al'ummar kasar mussaman da kasar ke kara fuskantar barazanar annobar. Magajin gari mace bakar fata ta farko a birnin Johannesburg Mpho Phalatse na taimakon 'yan sanda wajen rangadi don hukunta masu take dokokin.

Mpho Phalatse sabuwar jagorar birnin Johannesburg na Afirka ta KuduHoto: Adrian Kriesch/DW

Ko da yake an sanya dokar takaita zirga-zirga a dare, a don haka ne ya zama wajibi ga dukkan gidajen rawa su kulle a lokacin da ya kamata. Ana dai ganin akwai jan aiki a gaban Phalatse saboda yadda ake ganin zata kawo karshen koken rashin ababen more rayuwa da ake yi a birnin, sai dai kuma annobar cutar corona ka iya kawo cikas kan hakan.

A kokarinta na ganin cewa barazanar cutar a karo na hudu bai yi wa birnin illa kamar sauran na baya ba, magajin garin na kokarin wayar da kan al'umma kan mahimmancin yin allurar rigakafin cutar. Alkalumma na nuni da cewa mutum 1 kacal ne cikin hudu na al'ummar kasar suka yi cikakken rigakafin duk da cewa an samar da allurar. Sai dai har kawo yanzu mutane na ci gaba da nuna shakku kan allurar.

Hoto: Sumaya Hisham/REUTERS

Magajin gari Phalatse ta nuna damuwarta kan yadda al'umma ke yiwa allurar irin wannan mahaguwar fahimtar. Phalatse dai uwa ce kana kwararriyar likita da take fargabar ayyukan da suka shafi annobar corona ka iya mamaye duk lokutanta.